Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta amince Babban Bankin Najeriya (CBN) ya rufe asusun bankin wasu mutum 19 da suka jagoranci zanga-zangar #EndSARS.
Umarnin kotun ya ce bankuna za su rufe asusun ajiyan ne tsawon kwana 180 domin CBN ya kammala binciken da yake yi a kansu.
- Fitaccen mai yaki da ‘yan fashi, Ali Kwara ya rasu
- Kotu ta amince a ba wa Sarkin Zazzau sanda
- #EndSARS: Gwamnan Legas ya kai wa Buhari rahoton barnar da aka yiwa jiharsa
Tuni kotun ta umarci bankunan Access, Fidelity, First Bank, Guaranty Trust, UBA, da kuma Zenith, su rufe asusun mutanen, ciki har da kamfanin Gatefield kamar yadda tun ranar 20 ga Oktoba 2020 CBN ya bukata.
Ana iya tunawa kamfanin Gatefield ya yi karar bankin Access kan rufe masa asusu don an yi amfani da shi wajen daukar nauyin tallata zanga-zangar #EndSARS a kafafen yada labarai.
Masu asusun da za umarnin ya shafa su ne Bolatito Racheal Oduala, Chima David Ibebunjoh, Mary Doose Kpengwa, Saadat Temitope Bibi, Bassey Victor Israel, Wisdom Busaosowo Obi, da kuma Nicholas Ikhalea Osazele.
Akwai kuma Ebere Idibie, Akintomide Lanre Yusuf, Uhuo Ezenwanyi Promise Mosopefoluwa, Adegoke Pamilerin Yusif da Umoh Grace Ekanem.
Sauran su ne Babatunde Victor Segun, Mulu Louis Teghenan, Mary Oshifowora, Winifred Akpevweoghene Jacob, Victor Solomon, Idunu A. Williams da kuma kamfanin Gatefield.
Tun da fari dai kamfanin Gatefield yayi karar bankin Access kan rufe wani asusunsa da aka yi amfani da shi wajen tallata zanga-zangar #EndSARS a kafafen yada labarai.
Ana hasashen baya ga rufe asusun jagororin masu zanga-zangar akwai yiwuwar hana su fita kasashen waje har sai an kammala bincike a kansu.