Zaman dar-dar da ake yi a Jihar Legas sakamakon zanga-zangar#EndSARS, ya sa gwamnatin jihar ta umarci daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su zauna a gida.
Kwamishinar Ilimi ta jihar, Folasade Adefisayo ta ce kare lafiyar daliban, malamansu da sauran ma’aikatan makarantun na da matukar muhimmanci ga gwamnatin jihar.
Sai dai ta shawarci iyaye kan su kara sa ido kan yaransu ta hanyar tabbatar da cewa bata-gari ba su yi amfani da su wajen ta da zaune tsaye ba.
Kwamishinar ta kuma shawarci masu makarantu da su ci gajiyar tanade-tanaden da aka yi musu na karatu daga gida ta hanyar rediyo, talabijin da intanet, kamar yadda aka yi a lokclacin kullen coronavirus.
Ta ce nan ba da jimawa ba za su sanar da ranar sake bude makarantun da zarar kura ta lafa.