✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Gwamnan Legas ya kai wa Buhari rahoton barnar da aka yiwa jiharsa

A ranar juma’a gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gabatar masa da rahoton irin barnar da bata-gari…

A ranar juma’a gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gabatar masa da rahoton irin barnar da bata-gari suka yi a jiharsa

Fadar gwamnatin tarayya ta bayyana a shafinta na Twitter cewa shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan wanda kuma ya gabatar masa da rahoton yadda rikicin #EndSARS ya shafi jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne ministoci daga yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya suka bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki lamarin da ya faru a Lekki.

Sai dai shugaba Buhari ya bawa dukkan ministoci wa’adin mako guda kan kowannensu ya koma jiharsa don ya jawo hankalin mutanensa kan illar tashin hankali.

Lokacin da gwamnan Legas Sanwo-Olu ke nuna wa Shugaba Buhari hotunan barnar da aka yi wa jiharsa

Shugaban ya kuma umarci ministocin su gabatar da rahoton shirin da suka yi na kawo zaman lafiya a fadin kasa.

Zanga-zangar da aka faro ta domin neman kawo karshen zaluncin bangaren ‘yan sanda na SARS dai daga baya ta rikide inda bata-gari suka shiga satar kayan mutane tare da lalata dukiyoyin al’umma da na gwamnati a sassa daban-daban na Najeriya.

Sai dai gwamnatin tarayya na ganin cewa labarun karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun yi tasiri sosai wajen tada fitina a lokacin zanga-zangar.

Wanda hakan ne yasa gwamnati ta fara tunanin kafa dokar sanya ido akan kafafen sada zumuntar.