✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Ganduje ya nemi taimakon Rarara da Ali Nuhu

Ya bukaci Rarara da ya rera wakokin fadakar da jama'a kan muhimmancin zaman lafiya.

A kokarin Gwamnatin Kano na tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Ganduje, ya bukaci kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da mawaka su yi amfani da kwarewarsu wurin fadakar da jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata gana wa da ya yi a daren Talata da Kungiyar mawaka da ma su shirya fina-finan Hausa ta MOPAN, a dakin taro na Africa House da ke Gidan Gwamnatin Jihar.

Da ya ke gabatar da jawabinsa, Ganduje ya yi kira ga fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, da ya rera wakokin fadakar da jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.

Kazalika ya bukaci jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu daga bangaren masu shirya fina-finan Hausa, da ya shirya fina-finan wayar da kan al’umma kan fa’idar zaman lafiya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu karancin zaman lafiya a wasu jihohin Nijeriya sakamakon zanga-zangar #EndSARS da aka fara gudanar da ita makonni biyu da suka gabata.