✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EndSARS: Ganduje ya kafa kwamitin zaman lafiya

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin tabbatar da zaman lafiya a jihar bayan rikicin da zanga-zangar #EndSARS ya haifar. Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar,…

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin tabbatar da zaman lafiya a jihar bayan rikicin da zanga-zangar #EndSARS ya haifar.

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya sanar da haka bayan wasu bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar #EndSARS wurin tada hankalin mutane tare da barnata dukiyoyin a jihar.

A yayin da yake jawabi ga kwamitin, Ganduje ya ce dole kwamitin ya zage damtse domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.

Gwamnan ya yi tir da wadanda suka yi barnar suka kuma jefa jama’a cikin tashin hankali.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Boniface Ibekwe da Rev. Adeyemi Samuel, wanda dukkaninsu Kiristoci ne kuma jagorori a unguwar Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Fagge.

Gwamnan ya kuma yi irin wannan zaman da manyan malaman Musulunci da ke jihar ta Kano.