✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Falz ya kaurace wa taron gwamnati

Shahararren mawakin Najeriya, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz ya janye halartar taron da Gwamnatin Tarayya ta shirya ta bidiyo domin kawo karshen…

Shahararren mawakin Najeriya, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz ya janye halartar taron da Gwamnatin Tarayya ta shirya ta bidiyo domin kawo karshen zanga-zangar #EndSARS.

Karfe 3 na ranar Jama’a za a fara taron da Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa ta kira wanda Falz ke daga cikin masu jawabi.

“Ban amince in zama daga cikin masu yawabi ba. Bayanan bogi aka ba ni kuma babu bukatar taron.

“Abin bukata kawai shi ne #5for5 #SARSMUSTEND”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Jama’ar.

Da farko taron ya gayyato Falz; Shugaba ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu; jagoran zanga-zangar #EndSARS, Segun Awosanya; da Jami’in DAI a Najeria, Joe Abah a matsayin masu jawabi a taron.