Shahararren mawakin Najeriya, Folarin Falana wanda aka fi sani da Falz ya janye halartar taron da Gwamnatin Tarayya ta shirya ta bidiyo domin kawo karshen zanga-zangar #EndSARS.
Karfe 3 na ranar Jama’a za a fara taron da Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa ta kira wanda Falz ke daga cikin masu jawabi.
- Jama’a na da ’yancin bayyana ra’ayi —Shugaban ’Yan Sanda
- Yadda na yi gamo da kura a wajen neman kudi —Aminu Dantata
“Ban amince in zama daga cikin masu yawabi ba. Bayanan bogi aka ba ni kuma babu bukatar taron.
“Abin bukata kawai shi ne #5for5 #SARSMUSTEND”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Jama’ar.
Da farko taron ya gayyato Falz; Shugaba ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu; jagoran zanga-zangar #EndSARS, Segun Awosanya; da Jami’in DAI a Najeria, Joe Abah a matsayin masu jawabi a taron.