Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da almurun Alhamis kan matsalar tsaron da kasar ke ciki a halin yanzu.
Babban Hadimin Shugaban Kasa kan Watsa Labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan da yammacin Alhamis.
“Bayan zuzzurfar tattaunawar da ya yi da shugabannin tsaron kasa kan halin da kasa ke ciki, Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi yau [Alhamis] da misalin karfe 7 na yamma,” inji sanarwar.
A cewar sanarwar jawabin zai gudana ne da misalin karfe 7:00 na maraice ta gidan talabijin na kasa (NTA) da gidan Rediyon Tarayya na FRCN.
Jawabin shugaban na zuwa ne bayan da ya sha fuskantar matsin lamba kan daukar matakin da ya dace ko kuma yi wa ’yan kasa jawabi domin kwantar musu da hankula.
Tun kimanin makonni biyun da suka gabata Najeriya ke fama da zanga-zangar da ta fara da neman rushe sashen rundunar ‘yan sanda ta SARS.
Daga baya zanga-zangar lumanar ta rikide zuwa rikici, kashe-kashe, kone-kone da ma lalata rayuka da dukiyoyi a sassan kasar.