Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa dake da alhakin bincike kan yadda hukumar ‘yan sanda suke gudanar da ayyukansu, ya bayar da shawara kan hukunta wasu jami’an rundunar SARS 16 bisa zarginsu da aikata laifin kisan kai a wasu jihohin kasar nan 12 da birnin tarayya Abuja.
Tuni kwamatin ya mika wa Shugaban Kasa rahotansa kan jami’an da aka tabbatar sun zake har ta kai su ga yin kisa da aikata sauran miyagun laifuka na cin zarfin bil Adama.
- #EndSARS: ‘Yan sanda sun hana matasa dibar abincin tallafi
- An sake saka dokar hana fita a jihar Osun
Sauran wadanda kwamitin ya mika wa sakamakon binciken sun hada da Hukumar kula da ayyukan ’yan sanda ta Kasa da Sifeto Janar na ’yan sanda Muhammad Adamu da kuma Lauyan Koli na kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.
Daga cikin wuraren da abun ya shafa ya hada da birnin tarayya Abuja da Jihohin Kaduna da Gombe da Enugu da sauran su.
Wani rahoto ya ce tun Yunin shekarar da ta gaba ne kwamatin ya kammala bincikensa, inda ya zakulo wadanda ake zargi suna da hannu dumu-dumu a laifin kisan.