Yayin da zanga-zangar #EndSARS ke kara kazancewa, an shawarci ‘yan kasuwa daga Arewacin Najeriya da su dakata da zuwa Jihar Legas domin kasuwanci.
Babban limamin masallacin Juma’a na Sultan Bello dake Kaduna, Sheikh Muhammed Suleiman Adam Abubakar shine ya yi gargadin yayin hudubar sallar Juma’a.
- Rikicin Hausawa da Yarabawa ya barker a Legas
- ‘Labarun karya ne suka haifar da rikicin a Legas’
- #EndSARS: Yadda bata-gari ke sheke ayarsu a Legas
Sheikh Abubakar ya ce akwai gagarumin hatsari ga dukkan ‘yan kasuwar dake yankin Arewaci da suke safarar kaya daga yankin zuwa kudu ko su saro daga kudu zuwa arewa musanman jihar Legas da ta yi kaurin suna a zanga-zangar.
Babban limaman ya ci gaba da cewa lalata kayan gwamnati da ba kamfanoni masu zaman kansu da masu zanga-zangar suka yi abun damuwa ne kwarai da gaske.
Daga nan sai ya kira da gwamnatin tarayya da ta yi kokarin ganin ta biya diyyar duk wata barma da masu zanga-zangar suka yi ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu.