Zanga-zangar matasa masu kokarin ganin an kawo karshen rundunar tsaro ta SARS a jihar Edo na dada kazancewa bayan da fusatattun matasa suka kone ofisoshin ‘yan sanda har guda biyu a birnin Benin.
Kone ofisoshin na Ugbekun da Odogbo na zuwa ne sa’o’i kadan bayan wasu matasan sun fasa gidan yarin birnin tare dake sakin fursunoni da dama.
Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun yi yunkurin kone wani ofishin ‘yan sanda a kasuwar Oba amma sun fuskanci tirjiya daga jami’an ofishin.
Yunkurin jin ta bakin kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar, SP Chidi Nwabuzor ya ci tura sakamakon rashin daga wayar da ya yi.
A wani labarin kuma, masu zanga-zangar sun huce takaicinsu kan Kamfanin Daar Communication, mamallaka gidan Talabijin na AIT a birnin na Benin.
Wani ma’aikacin kamfanin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa Aminiya cewa cincirindon matasan sun lallata ababen hawa da dama dake harabar kamfanin.
“Ban san me ya sa suka dau wannan matakin ba. Mu ba gwamnati ba, kamfani ne mai zaman kansa kuma aikinmu muke yi,” inji majiyar.