✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ENDSARS: An kona bankuna uku a Legas

’Yan daba sun cinna wuta a wasu bankuna tare da fasa shaguna suna satar kaya

Yan daba sun cinna wuta a wasu bankuna uku da ke kan titin Admiralty a unguwar Lekki ta Jihar Legas.

Majiyarmu ta ce bankunan da aka kona a daren Laraba sun hada da bankin Polaris, Access da kuma GTB.

’Yan daban sun kuma fasa shaguna da wuraren kasuwanci tare da sace dukiyoyin da ke ciki.

Abun ya faru ne jim kadan bayan jami’an tsaro sun yi harbe-harbe a wurin zanga-zangar #ENDSARS a yankin.

Kwana uku ke nan da zanga-zangar lumanar ta soma kazancewa, wanda a yanzu ta rikide zuwa kashe-kashe da kone-kone a sassan kasar nan.

Kazancewar lamarin wanda a wasu wuraren ta kai ga kai wa jami’an tsaro hari ta tilastwa wa wasu jihohi dokar hana fita.