Yayin da zanga-zangar EndSARS ke kara kazancewa, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta janye jami’an rundunar da ke tsaron manyan mutane nan take.
Sakon Shugaban Rundunar, Mohammed Adamu ya aiken wa Mataimakan Sufeto Janar na Yankuna da Kwamishinonin ’Yan Sanda na Jihohi ya ce umarnin ya fara aiki ne nan take.
“Duk wani kwamanda ’yan sanda da ya saba umarnin zai yaba wa aya zaki.
“Duk dan sanda da aka kama yana kare wani babban mutun, dauke da makami ko ba makami, to da sanin kwamandansa kuma kwamandan zai fuskanci hukunci”, inji shi.
- EndSARS: Yadda bata-gari ke sheke ayarsu a Legas
- #EndSARS: Buhari ya ba masu zanga-zanga hakuri
- Mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara
Sanarwar ta ranar Laraba ta kuma umarci jami’an da umarnin ya shafa su gabatar da kansu ga Kwamishinonin ’Yan Sandan jihohi nan take domin sake musu wuraren aiki.
Sai dai ta ce umarnin bai shafi masu tsaron Gidajen Gwamnati, Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai ba.
Hakan na zuwa ne a yayin da zanga-zangar EndSARS ta rikide zuwa kashe-kashe da kone-kone da sace-sace da ma hare-hare a kan kadarorin gwamnati da na sauran jama’a.
Yayin da gwamantocin jihohi ke kokarin shawo kan lamarin ta hanyar sanya dokar hana fita, masu zanga-zangar kan bijire a wasu jihohin.
An samu rahotannin yadda masu zanga-zangar da suka bijire wa dokar ke kai wa jami’an tsaro da ofisoshinsu hari.
Wasu hotuna da suka rika yawo sun yadda masu zanga-zanga suka yi wa wasu jami’an ’yan sanda kisan gilla a wasu jihohi.
A wasu wuraren, jami’an tsaron na cikin tsaka mai wuya inda aka hana su tsare wadanda suka saba dokar hana fita.
Ana ganin hakan ya bayar da dama ga bata-garin da ke ta farfasa shaguna da sauran wurare suna sace dukiyoyi
- An kona ofisoshin ’yan sanda
Akalla ofisoshin ‘yan sanda guda 10 masu zanga-zangar suka kai wa hari a Jihar Legas inda suka kokkona su tare da lalatawa da sace kaya, har ma da kashe jami’ai a jihar Legas.
Ofisoshin ‘yan sandan da aka kona a jihar sun hada da na Idimu, Igando, Layeni, Denton, Ilenbe Hausa, Ajah, Amukoko, Ilasa, Cele out post, ofishin SARS da ke Ajegunle, Ebute-Ero Mushin (Olosan), Ojo da kuma Ajegunle.