✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS : A gaggauta binciken harbin Lekki – Amurka

Kasar Amurka ta yi kira da a gaggauta yin bincike kan zargin yin amfani da karfi fiye da kima da ake yi wa sojoji da…

Kasar Amurka ta yi kira da a gaggauta yin bincike kan zargin yin amfani da karfi fiye da kima da ake yi wa sojoji da kuma harbin masu zanga-zanga a unguwar Lekki a jihar Legas.

A wata sanarwa da Sakataren Wajen Kasar, Mike Pompeo ya fitar, Amurka ta bukaci a yi bincike musamman a harbin da ake zargin yi a Lekki ranar Talata.

Pompeo ya ce, “Muna maraba da bincike cikin gaggawa kan amfani da karfi fiye da kima da ake yi wa jami’an tsaro.

“Duk wadanda suke da hannu a lamarin ya kamata a hukunta su daidai da dokokin Najeriya.

“Amurka na matukar yin Allah-wadai da harbin masu zanga-zangar na Legas da ya kai ga kisa da kuma jikkata mutane da dama.

“Taruwa da damar fadin albarkacin baki ‘yanci ne da yake daga cikin ginshikan dimokradiyya da ya zama dole hukumomi su girmama shi.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda rikicin ya ritsa da su,” inji Mista Pompeo.