Fadar Elysée ta sanar da cewa Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron zai fara ziyarar kwana biyar a Nahiyar Afirka a ranar Laraba, inda zai sauka a Gabon, Angola, Kongo daga nan ya zarce Kongo-Brazzaville.
Macron na shirin halartar taron UNESCO kan kare gandun daji wanda ke gudana a Libreville, babban birnin Gabon.
- Abubuwan mamaki 10 a zaben shugaban kasa na 2023
- Rikici ya barke tsakanin masu bore kan sakamakon zabe a Abuja
Shugaban ya kuma shirya bude sabon Ofishin Jakadancin Faransa a birnin.
A Angola, babban batun da za a tattauna shi ne hadin gwiwa a fannin noma.
Wannan ya kamata ya kara samar da tsaro na kasa da kuma taimakawa manoma a can domin tunkarar matsalar sauyin yanayi.
A Jamhuriyar Kwango kuwa, ana sa ran za a mayar da hankali kan kulla alaka da Faransa.
Ziyarar ta Macron zuwa Afirka ta zo ne a daidai lokacin da Faransa a matsayinta na mai mulkin mallaka ke fuskantar matsin lamba a kasashen Afirka da dama.
Ana nuna bacin rai kan Faransa, alal misali, a kasashen Sahel, inda Faransa ke da sojoji a yaki da ta’addanci.
A ranar Litinin, kafin fara tafiyar, Macron ya sanar da janye karin sojoji daga Afirka.
Macron ya kuma ba da shawarar kafa doka don dawo da fasahar da aka sace a kasashen Afrika.