✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emefiele ya tabbatar min ba za a cire Ajami daga jikin Naira ba – Sanusi

Ya ce Gwamnan na CBN ne ya tabbatar masa da hakan

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya ce Gwamnan bankin mai ci, Godwin Emefiele, ya tabbatar masa cewar ba za a cire rubutun Ajamin da ke jikin takardar Naira ba.

Basaraken ya bayyana haka ne a matsayin martani ga jita-jitar da ake yadawa kan cewa bankin na shirin cire rubutun Ajamin da ke jikin kudin na Najeriya.

A ranar Larabar da ta gabata ce aka ji CBN ya ba da sanarwar shirinsa na sake tsarin takardun Naira da suka hada da N200 da N500 da kuma N1,000.

Bankin ya ce yana sa ran sabbin takardun kudin su soma aiki ya zuwa ranar 15 ga watan Disambar 2022.

Sai dai kuma tun bayan da bankin ya ba da sanarwar shirin nasa, ’yan kasa ke ta bayyana ra’ayoyi da tafka muhawara a kan batun.

Yayin da bankin ke ra’ayin ya dauki wannan mataki ne don daga darajar Naira da karfafa tattalin arzikin kasa, wasu ‘yan kasa kuwa na ganin hakan ba alheri ba ne ga kasa.

Wasu ma kallon lamarin suke da salo na yaki da addini.

Sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, Sanusi, wanda kuma tsohon Sarkin Kano ne ya yi kira ga shugabannin addini da su guji yada bayanan da ba a tantance sahihancinsu a cikin al’umma gudun haifar da akasi a tsakanin jama’a.