✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emefiele ya nemi kotu ta hana DSS bincikar sa

Emefiele ya nemi kotu ta yi watsi da zargin mallakar haramtattun makamai da DSS ke masa, hukumar kuma na adawa da belinsa da kotu ta…

Kotu ta sanya ranar Talata 15 ga watan Agusta da muke ciki a matsayin ranar sauraron bukata dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke neman hana gwamnati gurfanar da shi.

Kotun ta sanar da haka ne a zamanta na safiyar Juma’a, inda Emefiele ya bukaci ta yi watsi da zargin da hukumar DSS ke masa na mallakar haramtattun makamai.

Alkalin kotun, Nicholas Oweibo, ya ce lokacin da aka sanya zai ba da dama ga bangarorin su shirya martaninsu ga juna a shari’ar ta Emefiele da ke tsare a hannun DSS tun ranar 10 ga watan Yuni.

A ranar ce Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Legas za ta saurari bukatar hukumar tsaro ta DSS da ke tsare da Emefiele na neman kotun ta janye belinsa da ta bayar.

A zaman kotun na baya ne ta ba da belin Emefiele a kan Naira miliyan 20 da mutum biyu da za su tsaya matsa, inda ta bukaci a tsare shi a gidan yari sai ya cika sharuddan.

A yayin da ake shirin tafiya da shi gidan yari ne jami’an hukumar DSS suka murkushe takwarorinsu na hukumar gidajen yari a harabar kotu, suka yi awon gaba da shi, wanda hakan ya ja musu Allah-wadai.

Hukumar dai ta nesanta kanta da gaban kai da ta ce jami’anta suka yi, tare da alkawarin daukar mataki a kan duk wanda ta samu da laifin saba ka’idar aiki.

Sai dai zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gareta game da inda aka kwana.