Shugaban kamfanin kera motoci na Tesla kuma attajirin duniya, Elon Musk, ya yi tayin sayen dandalin sada zumunta na Twitter kacokam don ya “fito da” da baiwa ta musamman da kamfanin ke da ita.
Cikin wata sanarwa ta ban-mamaki, Mista Musk ya ce zai biya dala 54.20 kan kowane hannun jari daya, inda ya yi hasashen darajar dandalin kan dala biliyan 40.
- NLC ta bai wa Gwamnati wa’adin kwanaki 21 ta sulhunta da ASUU
- Osinbanjo ya bar jam’iyyar APC reshen Jihar Legas
A kwanan ne aka ruwaito cewa Musk ya zama mai mafi girman hannun jari a Twitter bayan ya kara yawan hannun jarinsa a kamfanin.
Ya kara da cewa idan ba a karbi tayin da ya yi ba: “Zan yi tunanin sauya matsayina na mafi yawan hannun jari.”
Wasu bayanai da ya mika wa hukumar kula da harkokin kudi ta Amurka sun nuna sakonnin da Musk ya tura wa majalisar zababbu na Twitter cewa ya yanke shawara a karshen mako cewa ya kamata kasuwancin kamfanin ya zama mai zaman kansa.
An gayyaci Mista Musk ya kasance cikin majalisar zababbun kamfanin amma Twitter ya sanar ranar Lahadi cewa ya janye tayin da ya yi masa.
Cikin bayanan, Musk ya ce ba ya son “je-ka-ka-dawo” sannan ya ce: “Tayi ne mai tsoka kuma masu hannun jarinku za su so shi.”
Musk ya ce zai dauki matakin sayar da hannun jarinsa na Twitter idan har ba a karbi tayin nasa ba.
“Wannan ba barazana ba ce, kawai dai ba zai zama zuba jari kai waye ba idan ba a samu sauyin da ake bukata ba,” in ji shi.