A kokarinsa na ganin an fifita samar da zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban a arewacin Najeriya, Shugaban Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya raba buhunan kayan abinci guda 50 ga zawarawan Kiristoci da marayu da sauran mabukata a yankunan sassan Kudancin Kaduna.
Malamin ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin matan su yi amfani da wannan damar ne wajen ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya tare da rokon Allah Ya kawo karshen halin rashin tsaro da kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
- Matawalle ya yi martani kan raba wa Sarakunan Zamfara motoci na alfarma
- A kori Minista da mashawarcin Buhari kan tsaro —’Yan Majalisa
El-Zakzaky ya ce hakan na daga cikin irin gudummawar da ya saba bayarwa duk shekara ga miliyoyin ’yan Najeriya da ke fama da matsalar hauhawar farashin kayayan abinci.
An fara raba kayayyakin abincin ne tun a makon jiya ga al’ummar Musulmi, inda zuwa yanzu aka fadada shi zuwa ga Kiristoci da ke yankin Kudancin jihar domin taimaka wa musamman mabukata, lura da irin halin da ake ciki.
Sheikh Zakzaky ce za su ci gaba da tallafa wa dukkanin Musulmi da Kiristoci da kayan abinci har tsawon wannnan wata na Ramadan da ake ciki.
Yayin da yake karbar abincin a gidansa kafin rabarwa, Fasto Yohanna buru na cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, ya bayyana farin cikinsa da godiya ga Sheikh Ibrahim El-Zakzaky saboda tunawa da Kiristoci musamman a halin da ake ciki na tsadar kayan abinci a kasuwanni.
Ya ce a a halin da ake ciki Kiristoci suna shirin kammala nasu azumin na kwana 40 wanda za su hada da bukukuwan Ista.
Fasto Yohanna Buru ya ce ba wannan ne karon farko da shehin ke aiko da abinci ga Kiristoci ba domin yaukaka zumunci da karfafa zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kiristoci a Kudancin Kaduna.