✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

[email protected]: Ayyukan El-Rufai abin koyi ne —Buhari

Buhari ya ce El-Rufai ya zarce tsara wajen gudanar da ayyukan ci gaba da ababen more rayuwa a fadin Jihar Kaduna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Jihar Kaduna na samun cigaba a karkashin Gwamna El-Rufai, duk kuwa da kalubalen da take fama da su.

Buhari ya bayyana cewa jajircewar Gwamna Nasir El-Rufai wurin samar da ayyukan ci gaba abin koyi ne ga shugabanni masu tasowa.

Buhari ya bayyana haka ne a sakonsa na taya El-Rufai murnar cika shekara 62 a ranar Laraba.

Ya yaba wa gwamna da cewa ya zarce tsara wajen gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin Jihar Kaduna.

Sakon na Buhari, ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ya yi wa El-Rufai fatan alheri da kariyar Allah gami da koshin lafiya da kwanciyar hankali.