✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai zai kori malamai 233 daga aiki kan takardun bogi

Za a wallafa sunayen malaman da aka gano da takardun bogi a shafin Gwamnatin Jihar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta kori malamanta 233 kan laifin amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Shugaban Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko na Jihar Kaduna (KADSUBEB), Tijjahi Abdullahi, ya ce nan gaba kadan hukumar za ta gudanar da jarrabawa ga malaman makarantun firamare da sakandare a jihar.

Tijjani ya ce korar duk malaman da ke amfani da takardun bogi ta zama dole domin hana su lalata ingancin bangaren ilimin jihar.

“Daga bayanan da cibiyoyin suka yi mana, malamai 233 daga cikin 451 da muka tantance suna amfani ne da takardun bogi. Akwai cibiya daya da ta nesanta kanta da 212 da daga cikin takardun bogi 233.

“Hukumar za ta kori malamai 233 da ke amfani da takardun bogi, sannan ta tura wa Ma’aikatar Shari’a takardunsu domin ta gurfanar da su a kotu,” inji shi.

Ya ce domin tabbatar da adalci, za a wallafa sunayen duk malaman da aka gano suna amfani da takardun bogi a shafin Gwamnatin Jihar Kaduna.

Shugaban na KADSUBEB ya ce domin tabbatar da adalci, za a wallafa sunayen duk malaman da aka gano suna amfani da takardun bogi a shafin Gwamnatin Jihar Kaduna.

Ya bayyana hakan ne a bayaninsa kan matakan da gwamnatin jihar take dauka domin bunkasawa da kuma inganta harkar ilimi a jihar.

A cewarsa hakki ne a kan hukumar ta tabbatar cewa malaman da ke koyarwa a makarantun gwamnin jihar sun cancanta kuma suna da sahihan takardun shaida.

A kan haka ne, a watan Afrilu ta kafa kwamitin tantance takardun da malaman suka gabatar domin tabbatar da suna da duk abin da ya dace a dauke su aiki a makarantun firamare da sakandare.

Ya ce hukumar ta tantance takardun malamai 451 ta hanyar tuntubar cibiyoyin da suke ce sun ba su takardun, tara daga cikinsu kuma suka amsa kira.

“Daga bayanan da cibiyoyin suka yi, malamai 233 daga cikin 451 suna amfani ne da takardun bogi. Daga cikin cibiyoyin akwai guda daya da ta nesanta kanta da takardu 212 daga cikin takardun bogi 233 da malaman suka gabatar,” inji shi.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da aikin tantance takardun malamai domin tabbatar da sahihancinsu.

A shekarar 2017 ne gwamnatin jihar ta dauki sabbin malamai 25,000, inda ta bayyana cewa za ta rika tantance su domin tabbatar da yadda suke samun ci gaban a aikinsu da kuma koyar da dalibai.