Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya tsige sarakunan Piriga da Arak — Jonathan Paragua Zamuna da kuma Janar Aliyu Iliyah Yammah (mai ritaya).
Kwamishinar kananan hukumomin jihar, Hajiya Umma Ahmad, ta sanar da cewa aikin sarakunan da aka tsige ya kawo karshe daga ranar Litinin.
- Direba ya murkushe ’yan uwan juna 4 har lahira a Jigawa
- An sako Dokta Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi daga kurkuku
A cewar sanarwar, “Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, zai kula da al’amuran Masarautar Piriga, har zuwa lokacin da za a nada sabon sarki, yayin da aka umarci sakataren majalisar masarautar da ya fara shirye-shiryen nadin sabon sarki.
“Gomna Ahmadu, Sakataren Majalisar Arak, shi ne zai kula da al’amuran masarautar tare jagorantar shirye-shiryen nadin sabon sarki.
“Gwamnati ba ta gamsu da bayanin Janar Iliyah Yammah kan tambayar da aka yi masa game da nadin hakimai hudu, sabanin wadanda aka amince da su a masarautarsa ba, da kuma dalilin rashin zamansa a Masarautar Arak.
“An tsige Jonathan Zamuna ne bayan rikicin kabilanci tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a Karamar Hukumar Lere, da kuma rashin zamansa a cikin masarautar.”
Sanarwar ta kuma sanar da sallamar hakiman kauyukan Aban, Abujan Mada da Anjil da ke masarautar ba tare da bata lokaci ba.
A karshen makon da ya gabata ne El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da korar baragurbin mutane da rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, har zuwa lokacin karewar wa’adin mulkinsa.
Gwamnan zai bar ofis a mako mai zuwa bayan ya yi wa’adi biyu a jere.