✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya kori magatakardar Majalisar Kaduna

El-Rufai ya ce zai ci gaba da tsige mutane daga mukamansu har zuwa lokacin da zai sauka daga mulki.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da korar Bello Zubairu Idris, magatakardar Majalisar Dokokin jihar.

Muyiwa Adekeye mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan.

Adekeye ya ce gwamnan ya kuma amince da sallamar Ya’u Yunusa Tanko, babban sakatare, da Francis Kozah, Sakataren Hukumar Bunkasa Kasuwanci ta Kaduna (KADEDA) daga aiki.

Ya kara da cewa gwamnan ya kuma amince da murabus din Stephen Joseph, babban sakatare a jihar.

A makon da ya gabata ne El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da rushe gidaje da kuma “korar baragurbin mutane daga mukamansu” har zuwa lokacin saukarsa daga mulki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da wani littafi kan abubuwan da ya gada.

Mista Emmanuel Ado, wani gogaggen dan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ne ya rubuta littafin mai suna, “Sanya Jama’a a Matakin Farko”.

Ya ce, “Duk wani abu mara kyau da muka samu, za mu cire shi, don kada gwamna mai zuwa ya sake yin hakan.

“A kula har zuwa 11 kafin lokacin da za mu bar ofis, ma mu ci gaba da korar miyagu tare da kawar da munanan abubuwa.”

Gwamnan ya bayyana haka ne kwana guda bayan da gwamnatinsa ta kwace ikon mallakar wasu kadarori tara na tsohon gwamnan jihar Ahmed Makarfi.