Gwamnatin Jihar Kaduna ta janye dokar hana sallah a masallatan khamsu salawat da coci-coci tare da ba da wajabta bin ka’idojin hana yaduwar cutar coronavirus.
A wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Mai Bai wa Gwamnan Shawara kan Watsa Labarai Muyiwa Adekeye ya ce janye dokar ya biyo bayan shawarar da Kwamitin Yaki da cutar a jihar ya bayar ne.
Wasu daga cikin ka’idojin da gwamnatin ta ce dole a rika bi sun hada da: sanya takunkumi da ba da tazara da wanke hannu a lokaci-lokaci da kuma kauce wa cinkoso da sauransu.
El-Rufai ya kuma yi gargadin cewa za’a rufe duk masallacin da ya ki bin dokoki ko ka’idojin da aka gindaya.
Idan ba’a manta ba gwamnatin jihar ta hana Sallah a masallatai ne tun a watan Maris na shekarar 2020 a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.