✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga Majalisar Dokokin Jihar

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 da ya kai Naira biliyan 257.9 ga majalisar dokokin jihar. Gwamnan ya…

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 da ya kai Naira biliyan 257.9 ga majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na shirin kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan wajen aiwatar da aiyuka da kuma a fannin Ilimi a jihar.

Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna Dakta Hadiza Balarabe, ce gabatar da kasafin kudin a madadinsa ta ce, kasafin na shekarar 2020 na da taken saka mutane a gaba wanda kuma hakan ya yi daidai da taken gwamnatinsa.

Ya kara da cewa, a cikin kasafin kudin karatun firemare da sakandire zai zama wajibi ga ko wani yaro dan jihar Kaduna kuma gwamnatin zata tabbatar da an yi amfani da wannan tsari ko kuma shirin gwamnatin domin ganin ko wane yaro ya samu ilimi a jihar.

“Shugaban Majalisar dokokin jihar Aminu Abdullahi Shagali, ya ce wannan kasafin kudin na shekarar 2020 ya kai Naira biliyan 257. 9 ‎. Kasafin an warewa sashen Ilimi Naira biliyan 64.64 (25.07 cikin 100), sashen lafiya kuma biliyan Naira 39.61 (15.36 cikin 100) sai aiyuka Naira biliyan 66.34 (25.72 cikin 100). Wannan ya nuna zamu mayar da hankali ne ga ci gaban dan adam da kuma gudanar da aiyuka,” in ji shi.

Mataimakiyar Gwamnan Kaduna lokacin da take gabatar da kasafin kudin shekarar 2020

Ya ce, gwamnatinsa ta bayyana aniyarta na fadada tare da bada dama ga Ilimi wanda hakan yasa aka fito da tsarin bada Ilimi kyauta kuma dole har sai an kammala sakandire ko makarantar koyan sana’oi.

A jawabinsa shugaban Majalisar dokokin jihar, ya yaba wa gwamnatin ne a bisa kasancewarsa na farko wajen fara biyan karancin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikatan ta.

Ya kuma jaddada aniyar ‘yan majalisar na bai wa gwamnatin jihar goyan baya domin a ciyar da jihar gaba.