Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2018 a gaban majalisar jihar.
Majalisar Zartarwar jihar ce a ranar 9 ga watan Oktoba ta amince da kasafin kudin, inda ta amince a gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa.
A kasafin kudin wanda ya kunshi kimanin Naira biliyan 216.5, kason muhimman ayyuka ya dauki kashi 60.54 cikin dari wanda ya kama Naira biliyan 131.1, sannan bangaren hakkokin ma’aikata ya dauki kashi 39.46 cikin dari wato Naira biliyan 85.4 ke nan.
Hakanan kuma, kasafin kudin ya bai wa bangaren ilimi kashi 25 cikin dari wanda ya kama Naira biliyan 33. Bangaren kiwon lafiya kuma ya samu kashi 12 cikin dari wanda ya kama Naira biliyan 17.5.
Hakanan kuma bangaren kyautata jin dadin al’umma ya samu Naira miliyan 941.5, yayin da bangaren muhalli ya samu Naira biliyan 3.455.
A jawabin gwamnan, ya dauki alwashin cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen cika alkawuran da ta dauka, sannan kuma ya yaba wa ‘yan majalisar bisa yadda suke aiki tukuru.
A nashi jawabin, shugaban majalisar, Aminu Shagali ya godewa wa gwamnan bisa yadda ya gabatar da kasafin kudin akan lokaci, sannan ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da bayar da gudunmuwarta wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da cigaba mai daurewa a jihar.