Gwamnatin Jihar Kaduna ta dawo da malaman makarantun firamare 1,266 da ta sallama a watan Yunin 2022 bakin aiki.
Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) ce ta sanar da haka a ranar Laraba ta bakin kakakinta, Hauwa Mohammed.
- Yadda aka yi jana’izar matar gwamnan Kano na farko Audu Bako
- Kotu ta daure barawon babur wata 9 a gidan yari
Sanarwar da ta fitar ta ce, “Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da a maido da malaman firamare 1,266 da aka kora bayan jarabawan gwajin da aka shirya masu a watan Yunin shekarar 2022.
“Bayan an saurari kokensu gwamnati ta amince da a dawo da malamai 392 da suka rubuta jarabawan suka kuma yi nasara da ma’aikatan gudanarwa 515 sai malamai 298 Wanda aka tabbatar da sun yi fama da rashin lafiya a lokacin jarabawar gwajin kuma suka kawo takardar shidar asibitin na hakika da ke dauke da bayanin likita.”
A cewarta, sauran wadnda da aka dawo da su sun hada da wadanda Sakatarorin Iliiminsu suka tabbatar da an sace su ko an yi garkuwa da su ko kuma sun yi hatsarin mota a lokacin jarabawar.
Ta kara da cewa duk da haka akwai wasu malamai 22 da aka cire sunansu daga tsarin biyan albashi saboda rashin gabatar da wata shaida kwakkwara da zai sa a saurare kokensu.
Ta bukaci malaman da aka dawo da su bakin aiki, da su je ofisoshin sakatarorin ilimin kananan hukumomin domin karbar takardun dawo da su bakin aiki.
A watan Yunin shekarar 2022 ne da gwamnatin jihar ta sallami malaman bisa hujjar cewa sun fadi jarawabar gwajin da musu mai cike da rudani.