✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya ba ma’aikatan Kaduna kwana 12 su yi rigakafin COVID-19

Gwamnatin ta ce bayan cikar wa’adin, masu shaidar rigakafin ne kawai za a bari su shiga ofis

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ba dukkan ma’aikatan jihar kwana 12 domin su yi rigakafin cutar COVID-19.

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Gwannan na Musamman a kan Harkokin Yada Labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a Kaduna.

Sanarwar ta ce daga karshen watan Oktoban 2021, dole kowane ma’aikaci a jihar ya nuna katin shaidar karbar rigakafin cutar kafin ya shiga kowace ma’aikata.

Har ila yau, sanarwar ta ce baki da suke son shiga wani ofishi ko wata ma’aikata a Jihar dole su tabbatar suna da katin rigakafin ko kuma shaidar yunkurin yin rigakafin daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar sanye da takunkumin rufe hanci.

A karshe gwamnatin ta shawarci jama’a da su hanzarta zuwa cibiyar bayar da rigakafin kafin cikar wa’adin.

Ko kafin gwamnatin Kaduna da ta bayar da umarnin, Jihar Edo ma ta ba da makamancinsa a watan da ya gabata, a daidai lokacin da adadin masu sake kamuwa da cutar yake dada hauhawa.