Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ba dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da ke sha’awar tsayawa takara nan da ranar 31 ga watan Maris, su ajiye mukamansu.
A ranar Talata ce dai Muhammad Sani Dattijo, Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, kuma tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.
- Buhari ya nemi gafarar ’yan Najeriya kan wahalar mai
- Yunwa za ta tagayyara mutanen Yemen matukar babu agaji —MDD
Aminiya ta gano cewa akwai wasu masu rike da mukaman siyasa da dama da ba su kai ga bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar ba tukunna.
Amma a cikin wata wasika da Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas Lawal, ya fitar, ta ce sabuwar Dokar Zabe ta 2022 wacce Shugaba Buhari ya rattaba wa hannu a kwanan nan, kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar, ta tanadi cewa dole masu rike da mukaman siyasa su ajiye mukamansu kafin zaben fid da gwani na jam’iyyunsu, muddin suna son tsayawa takara.
“Dokar ta yi tanadi karara cewa dole ne wadannan mutanen su ajiye mukamansu kwana 30 kafin ranar gudanar da zaben fid da gwanin kujerar da suke nema.
“Saboda tabbatar da cika wannan sharadin, dukkan masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan gwamnati a Jihar Kaduna da ke son tsayawa kowace irin takara, to dole ne su mika takardar ajiye aikinsu zuwa ga Sakataren Gwamnati, kafin nan da ranar 31 ga watan Maris, 2022,” inji wasikar.