Majalisar Koli ta Harkokin Shari’ar Muslunci a Najeriya (SCSN) ta caccaki Kungiyar Lauyoyin ta Kasa (NBA), bisa soke gayyatarta ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zuwa taronta na bana a matsayin mai jawabi.
Majalisar ta ce bambancin siyasa da addini sun makantar da shugabannin ‘NBA daga shika-shikan farko na aikin lauya’, yayin daukar matakin; saboda wasu ‘ya’yanta sun yi barazanar kaurace wa taron bisa zargin gwamnan da take hakki da kuma kasa magance kashe-kashe a Kudancin jiharsa.
“Wannan ra’ayin tsiraru ne ba wadanda suka san abin da ya dace ba, domin a fili yake cewa kungiyar na goyon bayan wani bangare a rikicin Kudancin Kaduna; Sabanin horon da ‘ya’yanta suka samu, take kuma da’awar kira gare shi na sauraron kowane bangare.
“Tsukakken ra’ayin siyasa da addini sun makantar da shugabancin NBA a lokacin yanke hukuncin, suka manta da manyan shika-shikan da aka horas da ‘ya’yanta akai.
“NBA ta nuna karara cewa tana goyon wani bangare a rikicin Kudancin Kaduna, sabanin horon da ‘ya’yanta suka samu take kuma horo da a yi [adalci], amma ba tare da sauraron bangaren da ake zargi ba”, inji sanarwar da Babban Sakataren NSCS Nafi’u Baba-Ahmed ya fitar.
“Janye gayyatar El-Rufai daga jerin masu jawabi a taron abun kyama ne da takaici daga fannin kwarewa da na shekara fiye da 40 ina alfahari da kasancewa a ciki.
“Abun nan ya zubar da kimar NBA da a baya take a matsayin muryar adalci da daidaito da kuma damuwa da abin da ya dami jama’a.
— Dakatar da El-Rufai ta bar baya da kura
Tuni dama matakakin ya bar baya da kura, inda Gwamna El-Rufai ya ce ko a gefen zaminsa, domin dama kungiyar ce ta bukaci ya sa albarka a taron.
Amma ya yi barazanar daukar matakin da ya dace kan bata masa suna da wanda ya rubuta takardar korafin da ke da nasaba da janye gayyatar.
Yayin da ake ta muhawara da nuna bacin rai a kai, kungiyar mabiya Shi’a ta IMN, wadda ba ta ga-maciji da El-Rufai, ta ce hakan ya yi daidai tana mai cewa gwamnan ya yi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.
A hannu guda kuma reshen NBA na Jihar Jigawa ya ce zai kauracewa yayin da wasu manyan lauyoyi suka yi kakkausan suka ga kungiyar da cewa tsabar rashin adalci ne.
Sanarwar reshen kungiyar na Jigawa ya ce idan har shaci-fadi ne abin dogara wajen yanke hukunci, to kamata ya yi NBA ta soke gayyatar da ta yi wa Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas daga cikin masu jawabi.
Ta ce akwai kwararan zarge-zarge a kan Wike wanda shi ma lauya ne, kan tauye hakki da saba doka, ciki har da rusa wuraren ibada ba bisa ka’ida ba.
Majalisar ta nuna damuwa game da shawarar da reshen NBA na Jihar Jigawa ya yanke na kaurace wa taron, “Kuma mun tabbata hakan da reshen ya yi abu ne da ya dace.
Ta ce don haka: “Ba za mu yi mamaki ba idan sauran rassan NBA na Arewacin Najeriya sun kaurace wa taron domin nuna rashin amincewa da abin da kungiyar ta yi, na ware gwamnan saboda gurguwar shawarar dakatar da gwaman ba.
“Ganin yadda kungiyar ta dauka ba tare da nuna kwarewa ba a kan rikicin ya zubar da kimarta. Sanin kowane cewa rikicin manoma da makiyaya dadadiyar matsala ce da ke ci wa kasar nan tuwo a kwarya.
“Ai a akalla kungiyar ta saurari gwamnan da masu zargin sa domin magance abun, amma ba ta biye wa wani bangare addini ko siyasa ba tare adalcin sauraron kowane bangare ba’, inji Majalisar.