Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yakar ’yan bindiga a fadin Jihar, babu maganar sulhu.
A martaninsa ga Sheikh Ahmad Gumi da ya bukaci a yi sulhu da ’yan bindiga a kuma biya su diyya, El-Rufai ya ce hanyar magance matsalar masu garkuwa ita ce kawai a yake su.
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
- Abin da ’yan bindigar Zamfara suka fada min —Sheikh Gumi
- Yadda aka sace matan aure bayan kashe ’ya’yansu a Kaduna
- Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa
“Duk wanda yake tunanin Bafulatanin da sai ya dade yake samun N100,000 bayan sayar da shanu, amma yanzu yana samun miliyoyi ta hanyar garkuwa da mutane, zai daina to ya yaudari kansa.
“Me ya sa za su kashe mutane su kone musu gidaje, wa ya taba su? Sheikh Ahmad Gumi abokina ne kuma abin da muka tattauna da shi ke nan.
“Na fada masa cewa da yawan Fulanin nan ba su san addini ba, don haka ban yarda da maganar da yake na a yafe musu ba,” a cewar El-Rufai.
El-Rufai, yayin da yake tattaunawa da Sashen Hausa na BBC, a ranar Litinin, ya ce yawancin Fulanin da ke garkuwa da mutane ba masu addini be ne, shi ya sa suke kashe mutane babu imani.
Game da yunkurin gwamnonin jihohi gomin kawo karshen matsalar, gwamnan ya ce, “Ba mu da hadin kai game da yakar ’yan bindiga, ni da gwamnan Jihar Neja ne kadai muke tattaunawa kan yadda za a kawo karshen ayyukan ’yan bindiga.
Aminiya ya yi kokarin jin ta bakin Dokta Gumi, game da matsayin na El-Rufai amma hakan ba ta samu ba.
Wayar malamin na kashe har zuwa lokaci da aka kammala hada wannan rahoto.