✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Clsassico: Gobe Madrid za ta kece raini da Barcelona

A gobe Asabar 21 ga wannan wata da muke ciki ne za a yi wasa mafi zafi a gasar rukunin La-Liga na Sifen na bana. …

A gobe Asabar 21 ga wannan wata da muke ciki ne za a yi wasa mafi zafi a gasar rukunin La-Liga na Sifen na bana.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 6 da kwata agogon Najeriya a filin wasa na Madrid da ake kira Santiago Bernebue.
Ba a Najeriya kadai ba, idan ana wannan wasa, miliyoyin ’yan kallo a sassan duniya ne suke natsuwa a akwatunan talabijin don su kalli yadda wasan zai kaya.  Hasalima a Najeriya gidajen kallon kwallo sukan cika makil ne a duk lokacin da ake wannan wasa.
Sai dai a wannan karo ana tababar ko shahararren dan kwallon FC Barcelona Lionel Messi zai buga wasan saboda jinyar da yake yi tun raunin da ya samu a watan Satumbar da ta wuce.  A goben ne ake sa ran dan kwallon zai dawo fagen daga, amma tuni Likitansa da ke Ajantina ya shawarce shi da kada ya kuskura ya ce zai buga wasan saboda hatsarin da ke tattare da hakan.  Likitan ya nuna idan dan kwallon ya sake fama raunin, to zai dauki lokaci mai tsawo yana jinya, kuma hakan ba karamin koma-baya ba ne gare shi da kuma kulob din FC Barcelona.  Sai dai rahotanni sun nuna tuni Messi ya fara yin atisaye da sauran takwarorinsa na Barcelona a shirye-shiryen buga wasan.
Kawo yanzu FC Barcelona ce take samun tebur a gasar da maki 27 daga wasanni 27 yayin da Real Madrid ke biye da maki 24.  Sai Atletico Madrid mai maki 23 a matsayi na uku yayin da Celta bigo ke matsayi na hudu da maki 21.
Idan Barcelona ta samu nasara a wasan, za ta ba Madrid tazarar maki 6 kenan, yayin da idan Madrid ce kuma ta samu nasara za ta dare kan teburin gasar duk da yake za ta hada maki daidai da na FC Barcelona wato maki 27 kenan.
’Yan kwallo biyu ne dai aka fi sanya wa ido a wasan, watau Cristiano Ronaldo na Madrid da kuma Lionel Messi na Barcelona.