✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Clasico: Jibi za a shawo ta tsakanin Barcelona da Real Madrid

A jibi Lahadi ce ake sa ran  za a yi wasa mafi zafi a gasar La-Liga ta Sifen inda manyan kungiyoyin kwallon kafa a gasar…

A jibi Lahadi ce ake sa ran  za a yi wasa mafi zafi a gasar La-Liga ta Sifen inda manyan kungiyoyin kwallon kafa a gasar FC Barcelona za ta kece raini da Real Madrid.

Wannan wasa, wanda ake yi masa lakabi da El-Clasico wato wasa mafi zafi, zai gudana ne a filin wasan  Barcelona na Camp Nou da misalin karfe 3:15 na rana agogon Najeriya.

Kimanin mutum miliyan 500 ne suke kallon wannan wasa a duk fadin duniya kai-tsaye ko a akwatunan talabijin da sauran kafofin watsa labarai.

Sai dai a wannan karo, za a yi wasan ne ba tare da shahararrun ’yan kwallon kulob din biyu ba, wato Lionel Messi na FC Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid.

Lionel Messi dai ya ji rauni ne a wasan da kulob din Barcelona ya yi da na Sebilla a ranar Lahadin da ta wuce, inda Barcelona ta doke Sebilla da ci 4-2. Kuma ana sa ran dan kwallon zai shafe mako uku yana jinya kafin ya koma fagen wasa.

Shi kuwa Cristiano Ronaldo ba zai yi wasan ba ne saboda ya canja sheka zuwa kulob din Jubentus na Italiya a karshen kakar wasan da ta wuce.Kawo yanzu kulob din FC Barcelona ne ke jan ragamar teburin La-Liga da maki 18 yayin da kulob din Real Madrid yake matsayi na 7 da maki 14.

Kulob din Madrid yana fuskantar kalubale a kakar wasa ta bana, kuma tuni magoya bayansa suka fara korafi kan yadda kulob din ya yi wasanni 6 a jere ba tare da ya samu nasara ba.

Idan FC Barcelona ya sake doke Madrid a jibi, ko shakka babu kulob din zai sake tsunduma cikin halin tasku, idan kuma Madrid ne ya samu nasara a wasan, zai dan farfado da martabarta a idon magoya bayansa.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo su cika makil don ganin yadda wannan wasa zai kaya.