✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-clasico: Gobe za a shawota tsakanin Madrid da Barcelona

A ci gaba da gasar rukunin Sifen da ake wa lakabi da La-Liga, a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a buga wasa mafi…

A ci gaba da gasar rukunin Sifen da ake wa lakabi da La-Liga, a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a buga wasa mafi zafi a gasar.  Za a yi wasan ne a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Sifen wato Real Madrid da kuma FC Barcelona a wasa karo na 17 a gasar ta bana.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na Santiago Bernebeu na Real Madrid da misalin karfe 1 na rana agogon Najeriya inda ake sa ran miliyoyin masoya kwallon kafa ne za su kalli yadda wasan zai kaya a daukacin duniya ciki har da Najeriya.

Wani rahoto ya nuna kimanin mutum miliyan 500 ne ke kallon wasan El-clasico a duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu da hakan ta sa ake ganin babu wani wasa da ya kai shi yawan ’yan kallo a fadin duniya a gasar rukuni-rukuni na kasashe. 

Kamar yadda tarihi ya nuna, kawo yanzu kungiyoyin biyu sun taba haduwa ne har sau 174 inda Real Madrid ta samu nasara sau 72 yayin da Barcelona kuma ta doke Madrid sau 69 sannan yi kunnen doki sau 33.

Sannan rahoto ya nuna kulob din Madrid ya samu nasarar zura kwallaye sau 283 a ragar Barcelona yayin da Barcelona kuma ta samu nasarar zura kwallaye sau 277.  Kenan za a iya cewa wasan gobe zai kasance na 175 a tsakanin kungiyoyin biyu da shi ma zai shiga cikin kundin tarihin kwallon kafa.

Kawo yanzu FC Barcelona ce take samun tebur a gasar ta La-Liga da maki 42 a wasanni 16 yayin da Real Madrid ke matsayi na 4 da maki 31 a wasanni 15 amma tana da kwantan wasa saboda halartar gasar FIFA Club World Cup da Madrid ta yi a Dubai inda kuma ta lashe kofin.

Magoya bayan kwallon kafar kungiyoyin biyu sun zuba ido su ga yadda wannan wasa na gobe zai kaya.  Hausawa dai na ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.