A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu, za a kece raini a tsakanin kulob din FC Barcelona da na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga na Sifen Wasan zai gudana ne a filin wasan FC Barcelona da ake kira Nou Camp da misalin karfe bakwai da rabi na dare agogon Najeriya.
A duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu duniya kan zuba ido ta ga yadda wasan zai kaya saboda muhimmancinsa. Duk da yake a wannan karo FC Barcelona ta ba Madrid tazarar maki 10 a teburin gasar ta La-Liga, magoya bayan kungiyoyin biyu suna ganin wasan ba zai yi armashi ba kamar yadda aka saba a kowace shekara, ganin cewa ko Real Madrid ta doke ta FC Barcelona babu abin da zai canza a matsayinta na mai jagorantar teburin gasar da maki 76 yayin da Madrid take matsayi na uku da maki 66 kafin wannan wasa.
Sai dai wasu na ganin idan Madrid ta samu nasara a kan FC Barcelona, to za ta farfado da hankoron da take yi na lashe gasar ganin cewa zai rage saura maki bakwai kenan a tsakaninsu ana ana saura wasanni bakwai a kammala gasar. Amma idan FC Barcelona ta doke ta Madrid, ko shakka babu sai buzunta don zai kasance FC Barcelona za ta ba Madrid tazarar maki 13 kenan a teburin gasar.
Sai dai ganin yadda Madrid take tashe a ’yan kwanakin nan musamman yadda take samun nasara a wasannin da take yi ya sanya wasu ke hasashen kulob din zai tabuka abin kirki a wasan na El-Clasico.
A wasan da kungiyoyin biyu suka yi a karo na farko kimanin watanni biyar da suka wuce, FC Barcelona ce ta bi Madrid har gida ta lallasata da ci 4-0.
Wasu magoya bayan kungiyoyin biyu a ciki da wajen Najeriya kan shiga yin caca a duk lokacin da wasa ke gudana a tsakanin kulob din biyu. A wannan karon ma wadansu tuni suka shiga cacar sanya wadansu muhimman abubuwa da suka hada da kudi da mota da gida da sauransu. Wadanda suka shiga irin wannan caca kan lashe ne idan kulob din da suke goya wa baya ya samu nasara.
Haka kuma gidajen kallon kwallo a Najeriya musamman a Arewacin kan cika makil saboda kashe kwarkwatar idanu. Da yawa daga cikin masu gidajen k=allon kwallon sun nuna sun fi samun kudin shiga a duk lokacin da kungiyoyin biyu ke fafatawa, don haka suke wasa wukarsu idan irin wannan wasa ya taso.
Wasu gidajen kallon ma kan samar da matakan tsaro, musamman ta bangaren bincikar masu shiga kallon da kuma wuraren ajiye ababen hawa.
El-Clasico: Gobe Barcelona za ta hadu da Real Madrid
A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu, za a kece raini a tsakanin kulob din FC Barcelona da na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga…