Hukuncin daurin rai-da-rai na iya rutsawa da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, muddin kotu ta kama su da laifin da ake tuhumar su na fataucin sassan jikin Dan Adam a kasar Birtaniya.
Hukumomin Birtaniya sun kama Sanata Ekweremadu da matarsa Beatrice ne kan zargin sun kai wani karamin yaro kasar da nufin cire kodarsa, domin a dasa wa ’yarsu mai fama da lalurar ciwon koda.
- Lafiyata kalau kuma Hamisu Breaker bai bani ko kwabo ba —Kamaye
- Mai neman takarar Sanatan Yobe ta Arewa ya maka Machina a Kotu
Kundin tsarin mulkin Birtaniya ya tanadi daurin rai-da-rai, wanda shi ne hukunci mafi tsauri, ga duk wanda aka samu da aikata laifin cinikin sassan jikin dan Adam.
Tuni jami’an tsaron Birtaniya suka gurfanar da ma’auratan a gaban kotu, inda alkali ya ba da umarnin tsare su ba tare da beli ba.
Kotun ta ba da umarnin ne bayan bullar wata wasika da ofishin Sanata Ekweremadu ya aike wa Offishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya, yana gabatar wa ofishin matashin cewa ya amince zai ba wa ’yarsu gudummawar kodarsa, wanda za a yi aikin dashen kodar a Birtaniya; Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar kuma zai dauki nauyin kudin jinya da tafiye-tafiyensu.
Amma ’yan sanda masu gabatar da kara sun bayyana wa kotun cewa su Ekweremadu sun yaudari hukumomin Birtaniya cewa za su kai yaron kasar ne domin ba shi rayuwa mai inganci, alhali kuwa sun kai shi ne domin su cire kodarsa.
Haka kuma, ma’auratan sun yi karyar cewa shekarun yaron 21, amma da aka gudanar da bincike sai aka gano cewa shekarunsa 15 ne kacal.
Sun kara da cewa dubun ma’auratan ta cika ne a filin jirgi na Heathrow da ke birnin Landan a kan hanyarsu ta zawa birnin Santanbul na kasar Turkiyya.
Ana zargin ma’auratan za su je kasar Turkiyya ne domin nemo wata kodar dan Adam da za a yi wa ’yar tasu dashe, bayan na ‘karamin yaron’ ya ki zuwa daidai da wadda ’yarsu ke bukata.
Dokar sassan jikin Dan Adam
Dokar kasar Birtaniya dai ta halasta bayar da gudummawa da kuma yin dashen sassan jikin dan Adam.
Duk da haka dokar ta haramta wa yara ’yan kasa da shekara 18 bayar da gudunmawar sassan jikinsu.
Dokar ta kuma ayyana sayen sassan jikin dan Adam a matsayin nau’in cinikin bayi, kuma babban laifi ne yin amfani da kudi domin samun amincewar mai bayar da gudunmawar.
A bisa dokar kasar, ana yanke wa masu laifin hukuncin daurin rai-da-rai.
Kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa watan Yuli Mai kamawa.