Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar Najeriya da su yi kaffa-kaffa yayin gudanar da bukukuwan Idin Karamar Sallar bana, kasancewa har yanzu ana fama da annobar Coronavirus a fadin duniya.
A cewar wata sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce a kan haka ne Shugaban Kasar zai gudanar da sallar idi tare da iyalansa da manyan jami’an gwamnatinsa a cikin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, suna mai kiyaye dukkan sharudan da dokokin yaki da cutar Coronavirus.
Kazalika, sanarwar da Malam Shehu ya fitar ta ce, Shugaba Buhari ya soke gaisuwar sallah da bisa al’ada shugabannin addinai da na al’umma da ma na siyasa suke kai wa Shugaban Kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ambato Shugaban Kasar yana mika godiyarsa ga Malamai na dukkan addinai da suka dag wajen yi wa kasar nan da al’ummarta addu’o’i na fatan alheri.
Shugaban Kasar ya kuma ribaci wannan dama ta mika sakon ta’aziyyarsa ga wadanda suka yi rashi na wasu daga cikin ’yan uwansu a sakamakon rikice-rikicen da suka rika faruwa a wasu sassan kasar.
Shugaba Buhari yana kira ga shugabannin al’ummomi da su gargadi matasa a kan hadarin da ke tattare da duk wani yunkuri na tayar da fitina.
Babu shakka ganin jinjirin watan Shawwal ne zai kawo karshen Azumin watan Ramadan da al’ummar Musulmi ke kwashe tsawon wata daya suna yi a kowace shekara da kuma gudanar da bikin Karamar Sallah wato Idil-Fitr kamar yadda addinin ya tanadar.
Tuni dai Majalisar Koli ta Musulmi a Najeriya bisa jagorancin Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad III, ta bayar da umarnin fara dubaa watan daga ranar Talata.
Idan ba a samu ganin watan ba a ranar Talata, hakan na nufin za a yi azumi 30, kana a yai sallar a ranar Alhamis wadda za ta kasance 1 ga watan Shawwal.