Akwai yiwuwar Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙi (EFCC) za ta gudanar da tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, kan zargin ruf-da-ciki kan Naira tiriliyan ɗaya da biliyan 300, a ranar Talatar nan.
EFCC na zargin Okowa da karkatar da kuɗaɗen ne daga kason 13% na kuɗaɗen ɗanyen mai da da warware don bunƙasa yankuna masu arzikin mai ma Nijeriya, a lokacin da yake Gwamnan Delta.
Okowa shi ne ɗan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na babbar adwa ta Jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023a Nijeriya.
A ranar Litinin ne EFCC ta tsare, ta ci gaba da yi masa tambayoyi a ofishinta da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
- Gwamnatin Tarayya ta soke kwangilar aikin titin Abuja-Kaduna
- Ku daina tsine wa shugabanni, ku bar su da Allah — Sarkin Musulmi
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar cewa, “Tabbas Sanata Ifeanyi Okowa yana hannunmu, muna tsare da shi.”
Majiyoyi a Hukumar sun bayyana cewa tsohon ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasan na Jamiyyar PDP, ya jima yana zuwa ofishin EFCC amsa tambayoyi, kafin a ƙarshe ta tsare a ranar Litinin.
Ana sa ran ranar Talata hukumar za ta gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin karkatar da kuɗaɗen.
Wasu ’yan cikin gida a hukumar sun bayyana cewa an faɗaɗa binciken zuwa kan wasu manyan jami’an Ma’aikatar Kudi da na Hukumar Bunƙasa Yankuna Masu Arzikin Ɗanyen Mai (DESOPADEC) da suka ya aiki a zamanin mulkin Okowa a Jihar Delta.
Wasu jami’an EFCC sun ce a halin yanzu hukumar tana bincikar ’yar Okowa, Marilyn Okowa-Daramola, mai wakiltar yankin Delta ta Arewa maso Gabas a majalisar dokokin Jihar, a sakamakon takardar ƙorafe-ƙorafe da aka shigarta kan mahaifinta.
Ana zargin tsare tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa ya kaɗa hantar ’yan siyasa da dama a Jihar Delta, inda ake ci gaba da jiran ganin yadda za ta kaya.