Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura da matarsa kan zargin rashawa.
Rahotanni a ranar Laraba sun tabbatar da cewar yanzu haka ana rike Al-Makura da matarsa a ofishin EFCC da ke Birnin Tarayya Abuja.
- Mutum 5 sun mutu bayan fashewar bam a Jamus
- ‘Buhari ya fi shekara 40 yana zuwa Landan a duba lafiyarsa’
Bayanai sun ce hukumar ta cafke Sanata Al-Makura kan zargin yadda aka karkatar da akalar wasu kudade a lokacin da ya mulki Jihar Nasarawa na tsawon shekara takwas.
Al-Makura ya mulki Nasarawa daga shekara ta 2011 zuwa 2019 kafin daga bisani ya tafi Majalisar Dattawa a matsayin Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.
Sai dai ya zuwa yanzu EFCC ba ta fitar da wata sanarwa dangane da cafke tsohon gwamnan ba.