✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta tsare shugaban hukumar alhazzai ta kasa

Tun ranar Talata shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa yake tsare a hannun EFCC

Hukumar Yaƙi da Masu Yi yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta ce tana tsare da Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Malam Jalal Arabi.

EFCC ta tsare Jalal Arabi ne a ci gaba da binciken da take gudanarwa kan zargin badaƙalar kuɗaɗen alhazan da sukansauje farali a 2024.

Kakakin EFCC, Dele Oluwale, ya tabbatar cewa tun ranar Talata shugaban hukumar aikin Hajji, Malam Jalal Arabi na hannun EFCC, amma ya ki yin karin bayani.

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ƙarƙashin jagorancin Jalal Arabi na fuskantar zargin almubazzarancin Naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar na tallafi ga maniyyata aikin Hajjin 2024.

Ana zargin NAHCON da karkatar kuɗaɗen, wadanda gwamnati ta bayar domin cika wa maniyyata kuɗin kujerar Hajji.

Hakan ya biyo bayan rokon tallafin da shugaban hukumar NAHCON ya yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan tashin Dala da ya sa aka samu babban gibi a kan kuɗaɗen kujerar da hukumar ta riga ta sanar.

A makon da ya gabata ne EFCC ta tisa keyar wasu manyan jami’an NAHCON daga ofisoshinsu zuwa na domin yi musu tambayoyi kan zargin badaƙalar karkatar da kuɗaɗen.

Wasu rahotanni na riya cewa EEFCC ta kwato Riyal 314,000 daga hannun jami’an hukumar aikin hajjinbda ake zargi da kuma shugabanta.

A karshen watan Yuli EFCC ta gayyaci Shugaban NAHCON Jalal Arabi zuwa ofishinta, inda ya amsa tambayoyi.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa babu inda aka karkatar da kuɗaɗen, domin kuwa, duk alhajin jiha da ya sauke farali a 2024 ya amfana a Naira na cikin kudin kujera.