Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta titsiye tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan zargin badakalar kudaden fansho.
Rahotanni sun ce hukumar ta gayyace shi ne bayan wani korafi da wasu ’yan fanshon suka kai gabanta.
- Fursuna ya dawo gidan yarin da ya tsere bayan shekara 30
- ‘Babu wanda ya isa ya yi babakere a shugabancin Najeriya’
Wani jami’i a hukumar ya tabbatar wa Aminiya cewa Sanata Kwankwaso ya amsa gayyatar ta EFCC, inda ya ce, “Yana amsa tambayoyi ne kan jerin korafe-korafen da aka shigar a kansa kan zargin yin babakere a kan kudaden fansho lokacin da yake Gwamnan Kano.”
A daya daga cikin irin wadannan korafe-korafen dai, ana zargin tsohon Gwamnan na Kano da karkatar da kudaden na ’yan fansho wajen gina gidaje da yawansu ya kai Naira biliyan 10, amma ya sha musanta hakan.
Har yanzu dai EFCC ba ta magantu ba a kan lamarin, amma a baya ta ce tana tuhumarsa ne kan wasu kudaden Kananan Hukumomin Jihar da yawansu ya kai N3.08bn.