Wani Babban Kotun Birnin Tarayya Abuja ya bayar da umarni ga Hukumae EFCC ta kwace kadarori mallakar Uwargidan tsohon Shugaban Kas Goodluck Jonathan na wucin gadi kafin a gama shara’a.
Mai shara’a Nnamdi Dimgba ne yanke wannan hukunci a ranar Litinin, sannan ya ce wannan hukunci zai yi amfani na kwana 45, wanda Hukumar EFCC ta za yi amfani da shi wajen kammala binciken da take yi.
Lauyan EFCC, Benjamin Mangi ne ya gabatar da bukatar kwace kadarorin a gaban kotu. Kadarorin su ne: Gida mai lamba 1758 yankin Cadastral B06 Mabushi, da kuma mai lamba 1350 A00 cikin birnin Abuja.
A nasa bangaren, lauyan Patience Jonathan Mike Ozehome (SAN), ya bukaci kotun da kada ta amince da bukatar lauyan na EFCC, domin a cewarsa, akwai wata shara’ar da ake yi a ita kotun game da kadarorin.
Hakanan kuma lauyan ya sanar da kotun cewa wata hukumar Gwamnatin Tarayya ta rushes ashen ginin da ake shara’a a kai duk da cewa maganar na kotu.