✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kwace fasfon Sadiya da Betta Edu

Ana zargin su da yin sama da fadi da makudan kudade a ma'aikatar.

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar.

Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadiya ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken.

“Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu.

“Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar.

Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata.

Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta.

Aminiya ta ruwaito cewa Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa tambayoyi kan zargin almundahanar kudi da ake mata.

Wannan na zuwa ne bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Edu ta bukaci babban Akanta-Janar na Tarayya ya biya Naira miliyan 585 da aka ware wa marasa galihu zuwa wani asusun banki na daban.

Bayan matsin lamba da ’yan Najeriya suka yi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Edu da kuma ayyukan ma’aikatar.

A nata bangaren kuma, Sadiya Umar-Farouq, tsohuwar minista a lokacin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ita ma EFCC ta gayyace ta domin amsa tambayoyi kam zargin da ake mata na sama da fadi da sama da biliyan 37.