Hukumar EFCC mai Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, ta cafke tsohon Gwamnan Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed.
Kakakin Hukumar, Mista Wilson Uwujaren ne ya inganta wannan rahoto cikin wani sakon kar ta kwana da ya aike wa manema labarai a ranar Litinin.
- Zan kawo hargisti a zaben 2023 — Igboho
- Sheikh Dahiru Bauchi ya amince da nadin Sanusi Khalifan Tijjaniyya
Sai dai Mista Uwujeren bai yi wani karin bayani ba doriya a kan na kama tsohon gwamnan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Hukumar za ta yi wa tsohon Gwamnan titsiye ne kan zarginsa da almundahana da dukiyar al’umma a lokacin da yake rike da madafan iko.
Alhaji Abdulfatah shi ne Gwamnan Jihar Kwara na tsawon wa’adi biyu daga shekarar 2011 zuwa 2019.
Ana iya tuna cewa, a watan Dasumbar 2020 ne Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon Gwamnan domin yi mata karin haske kan wasu harkallar kudi da kuma hukunce-hukunce da ya rika zartaswa a lokacin da yake gwamna.
Wannan shi ne karo na biyu da tsohon Gwamnan yake shiga hannun Hukumar tun bayan barin kujerar gwamnati a shekarar 2019.