Hukumar Yaki da yi wa Tattakin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta kama tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.
Aminiya ta gano cewa EFCC ta tsare tsohon Gwamnan ne a Babban Birnin Tarayya Abuja da yammacin ranar Talata.
- Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa
- Rikicin kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar hana fita
Hukumar dai na zargin Okorocha wanda ya jagoranci jihar ta Imo tsakanin shekarun 2011 zuwa 2019 ne da almundahana da kuma karkatar da kudaden jihar, ko da yake ya sha musanta hakan a baya.
Gwamnatin jihar dai karkashin jagorancin Hope Uzodinma dai sai da ta rufe wasu daga cikin kadarorin matars Rochas din da ake zarginta da samunsu ta haramtacciyar hanya.
Kazalika, a watan Fabrairu ma sai da aka tsare tsohon Gwamnan a ofishin ’yan sanda saboda wata ba-hammata-iska da ya yi da wasu jami’an gwamnatin jihar bisa kwace wasu daga cikin kadarorin matar tasa.
Sai dai daga bisani an saki Mista Okorocha bayan ’yan sa’o’i da kama shi.
Wannan ne dai babban kamu da EFCC ta taba yi tun bayan da Abdurrashid Bawa ya dare kan shugabancinta.