Ofishin Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ke Minna, Jihar Neja, ya kama mutane tara da ake zargi da damfara ta intanet.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar na Facebook ta ce an kama wadanda ake zargin ne bisa bayanin sirri da al’ummar unguwar da suke zaune suka bai wa jami’anta.
Sanarwar ta kuma ce EFCC ta kama wadanda ake zargin ne a wani otal, a bayan gidan man NNPC da ke garin Minna, kan zargin yaudara ta fuskar soyayya da sauran laifukan zamba.
Ta ce abubuwan da aka karba daga hannun matasan masu shekaru 20 zuwa 29 sun hada da mota daya kirar Toyota Venza da laptop da kuma wayoyin hannu na alfarma.
Hukumar ta ce za ta gurfanar da su gaban kotu da zaran ta kammala binciken su.