Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta tsare wasu tsofafin manyan jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) kan zargin badakalar kudade da yawansu ya kai Dala biliyan 7.2.
Jami’an EFCC sun tsare tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isah da kuma tsohon Manajan-Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, kan zargin almundahanar.
Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar ta tsare tsoffin manyan jami’an na NNPC ne kan zargin wadaka da kudaden gyaran matatun mai da ke Kaduna da Warri da kuma Fatakwal.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga kakakin EFCC, Dele Oyewale, amma jami’in bai amsa duk kiraye-kirayen da aka yi masa da kuma rubutattun sakon da aka tura masa domin samun bayani a hukumance.
Umar Ajiya ya kasance mai kula da harkokin kula da kudaden gyaran matatun guda uku da kuma da kuma manyan jami’an da ke aiki.
- Iran ta kama ’yan leƙen asirin Isra’ila 6
- Iyalan Kanawa da aka kashe a Uromi sun zargin gwamnati da yin watsi da su
Wani jami’in EFCC ya bayyana cewa hukumar tana kuma bincikar was jami’an NNPC da ke kula da wasu muhimman ayyuka kan zargin su da karkatar da kudade da kuma karbar na-goro daga ’yan kwangila.
A cewarsa, wadanda binciken ya shafa sun hada da Manajan-Daraktan Matatar Warri, Tunde Bakare; tsohon Manajan-Daraktan Matatar Fatakwal, Ahmed Adamu Diko da wani tsohon Manajan-Daraktan matatar, Ibrahim Monday Onoja.