✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama Manajan banki kan boye sabbin kudi na miliyan 29

Dama CBN na zargin wasu bankunan da yi masa zagon kasa

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC sun kama wani Manajan banki saboda zarginsa da boye sabbin takardun kudin da suka kai na Naira miliyan 29.

’Yan Najeriya da dama dai yanzu haka na fuskantar karancin kudi inda dubban mutane suke dogayen layuka a bankuna da wuraren cirar kudi na ATM domin samu kudaden.

Sai dai lokacin da yake sanar da tsawaita wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya yi zargin wasu bankunan kasuwanci na yi wa harkar raba sabbin kudaden zagon kasa.

Kwatsam sai ga shi a ranar Litinin, Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya sanar da cewa hukumar ta baza jami’anta a cikin bankunan Abuja.

A nan ne ya ce jami’an sun kama Manajan bankin saboda yadda ya hana a zuba kudi a na’urar ATM ta bankin, duk kuwa da cewa suna da tsabar sabbin kudi har Naira miliyan 29.

Ya ce bayan sun gano badakalar, sun tabbatar da an raba dimbin mutanen da suka taru a layi kudaden, sannan aka kama Manajan.

Wilson ya ce, “Wannan ya nuna karara irin zagon kasan da bankuna ke yi wa manufar gwamnati ta sauya fasalin kudaden.

“Mun ziyarci sama da bankuna biyar, kuma yanzu haka muna irin wannan ziyarar a sauran ofishin shiyya na hukumar.

“’Yan Najeriya na shan matukar wahala wajen samun kudadensu a bankuna, don haka duk mai korafi ya kai kokensa wajen hukumarmu,” in ji sanarwar ta EFCC.