Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙi (EFCC) ta tsare jami’an gwamnatin jihar Katsina guda biyar kan zargin karkatar kuɗaɗen tallafin hukumomin duniya da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 1.29.
Hukumomin lafiya na duniya ne suka sanya kuɗaɗen a asusun gwamnatin jihar Katsina, amma jami’an da ake zargin suka yi sama da faɗi da su.
Jami’an da suka shiga hannu ma’aikata ne a Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Jihar Katsina, kuma ƙarshen mako EFCC ta cika hannunta da su.
Kakakin EFCC na ƙasa, Dele Olukoyede, ya ce an kama sune bayan takardar ƙorafin da gwamnatin Kastina ta aike wa hukumar na zargin su da karkatar da kuɗaɗen.
- ’Yan ɗaurin aure 19 daga Kano sun rasu a hatsarin mota a Filato
- NAJERIYA A YAU: “Wannan Ce Ɗaya Daga Cikin Ummul Haba’isin Lalacewar Najeriya”
Dele Oyewale, ya ce kuɗaɗen Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO) da Kungiyar Likitoci ta Duniya (MSF) da Ƙungiyar Likitoci Aiki da Cikawa ta likitocin Duniya (ALIMA) su sanya a asusun gwamnatin jihar Katsina ne mutanen suka yi aown gaba da su.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da kuma Nura Lawal Kofar Sauri.