Ofishin Hukumar EFCC shiyyar Ibadan ya cafke wani mai hada-hadar kudaden Bitcoin bisa zargin sa da zambar kudi ta intanet.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce an kama dan kasuwar ne da kudaden bitcoin din tare da wasu mutane hudu.
- Irin ‘wulakancin’ da masu haihuwa ke fuskanta daga malaman asibiti
- ’Yan bindiga sun kashe daliban Jami’ar da suka sace Kaduna
- Ahmed Musa ya ba da N2m a gina masallaci a Kano
Ya ce an kama mutanen da ake zargi da aikata zambar ne a wurare daban-daban a yankin Elebu na garin Ibadan.
A cewarsa, mutanen da ake zargin, shekarunsu 21 zuwa 37 ne, kuma ana tuhumar su ne da hannu a yin zambar kudade ta intanet.
Uwujaren ya ce, an kwato motoci biyu da kwamfuta kirar laptop da wayoyin hannu da wasu muhimman takardu a hannunsu.
Kakakin hukumar ya ce za a gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu idan aka kammala bincike.